Sanatan da ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Shehu Sani ya fito ya na koka wa game da halin da wadanda aka yi garkuwa da su su ke ciki.

Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa ‘yan bindigan su kan yi lalata da duk wadanda tsautsayi ya rutsa da su, su ka fada hannun wadannan miyagun mutanen.

Shehu Sani yake cewa baya ga dukan tsiya, ‘yan bindigan su na amfani da wadanda su ka cafke.

‘Dan majalisar ya bayyana cewa wannan mummunan lamari ya na auku wa ne a kowace rana, a cewarsa, babu ranar da za ta wuce da ba ayi wannan ta’adi ba.

Ganin har yanzu ba a ceto yaran makarantar da aka sace ba, Sani koka da cewa tashin hankalin da daliban nan su ke ciki a halin yanzu, ba zai iya misaltu wa ba.

Fitaccen ‘dan gwagwarmayar da ya shiga siyasa ya bayyana wannan a shafin Twtter, ya na kiran gwamnati ta ceto daliban makarantar gandun noma d aka sace.

“Idan ‘yan bindiga su ka yi ram da mutane, ba ajiye su su ke yi cikin jin dadi har sai an biya kudin fansar su ba. Su na ci masu zarafi ne, su yi amfani da su kullum.”

Sanata Sani ya cigaba jawabinsa a dandalin Twitter: “Wani irin yanayi na tashin hankali da ba za iya tunani ba wadannan Bayin Allah su ke shiga a kowace sa’a.”

“Dole ayi duk abin da za ayi domin a ceto ‘daliban makarantun gandun daji.” Inji Shehu Sani.

Kwanakin baya kun ji yadda satar ‘daliban makarantar GSS Kagara ya jawo Shehu Sani da Gwamnan Neja su ka yi musayar kalamai a shafukansu na Twitter.

Gwamna Sani Bello ya maida wa tsohon Sanatan martani bayan ya ba shi shawara, gwamnan ya ce zai fi kyau ace Sani ya yi amfani da damar da ya samu a majalisa.

Mun fahimci cewa daga baya Sani Bello ya yi maza, ya goge wannan magana da ya yi.

Leave a Comment

%d bloggers like this: