Ahmad Babba Kaita, sanata mai wakiltar gundumar Katsina ta Tsakiya, ya jajantawa wadanda gobarar da ta lakume wasu sassan babbar kasuwar birnin ta shafa.

Daily Trust ta rahoto cewa, ya ba da gudummawar Naira miliyan 20 don ragewa ‘yan kasuwar da abin ya shafa asara. Ya bayar da gudummawar ne lokacin da ya kai ziyarar jaje ga ‘yan kasuwar a ranar Asabar.

A nasa martanin, shugaban kungiyar ‘yan kasuwar, Alhaji Abbas Labaran Albaba, ya jinjinawa sanatan kan wannan karamci, da kuma duk sauran masu jajantawaa da ke zuwa rukuni-rukuni da kuma daidaiku don ba da gudunmawarsu.

Leave a Comment

%d bloggers like this: