Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Charles Soludo, ya ce an yi musayar wuta tsakanin ƴan bindiga da ƴan sanda na tsawon mintina 15 da suka kai mishi hari

Charles Soludo, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya yace a harin da ƴan bindiga suka kai masa, sai da suka yi ta musayar wuta da ƴan sanda na tsawon mintuna 15.

Jaridar The Cable ta bayyana yadda wasu ƴan bindiga suka kaiwa Soludo farmaki a wani dakin taro dake Isuofia, ƙaramar hukumar Aguata dake jihar Anambra a ranar Laraba.

Wasu ƴan sanda guda 3 da suke kula da lafiyarsa sun rasa rayukansu a harin, sannan sun yi garkuwa da wani kwamishinan jihar, Emeka Ezenwanne.

“Sai da naji mutane suna ihu suna guje-guje don neman tsira. Sai da aka yi mintuna akalla 15 ana fafatawa da harbe-harbe suka tsaya.

“A lokacin da muka dawo sai muka ga gawar ƴan sanda uku a ƙasa cikin jini. Muna musu fatan rahamar Ubangiji,” cewar Soludo.

 

Leave a Comment

%d bloggers like this: