Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, IGP Muhammad Abubakar Adamu ya bada umarnin tura karin kayan aiki na bincike don tallafa wa ayyukan bincike domin ceto daliban da aka Sace a Kankara da kewayenta a jihar Katsina.

Hakan ya biyo bayan mummunan harin da wasu mutane dauke da muggan makamai suka kai makarantar sakandaren kimiyya ta Gwamnatin jihar Katsina a ranar Juma’ar data gabata wato 11 ga Disamba, 2020.

an tura jami’an da zasuyi bin cike da suka hadar da sojojin, da jami’an ‘Yan Sanda masu binciken kwakwaf daga Ofishin Leken Asiri ‘Force Intelligence Bureau wanda zasuyi aiki da rundanar ‘yan sandan jihar Katsina domin gano inda daliban suke.

Kawo yanzu Bincike na nuni da cewa an kashe daya daga cikin maharan tare da jikkata wani dan sanda yayin harin, sai dai ba’a gano adadin daliban da suka bata ba har kawo yanzu.

Leave a Comment

%d bloggers like this: