Rundunar yan sandan jihar Akwa Ibom ta samu nasarar hallaka wasu mutane huɗu da ake zargin yan fashin teku ne

Wasu mutane huɗu da ake zargin yan fashin teku ɓe sun gamu da ajalinsu a wata musayar wuta da suka yi da rundunar yan sandan Marine ƙaramar hukumar Oron, jihar Akws Ibom.

An kashe waɗanda ake zargin ne a wani sintiri da jami’an suka fita a Ikang Creek bayan samun bayanai akan yan fashin kamar yadda Punch ta ruwaito.

A wani jawabi da kakakin yan sandan jihar, Odiko Macdon, ya fitar ranar Laraba, wanda ya yi ma take da “Tsaftace hanyar ruwa a jihar Akwa Ibom” ya ce, sun kwato jirgin ruwa mai tsananin gudu da lamba 115HP, bindigu guda biyu, da kuma harsasai dag hannun mutanen.

A bayanin kakakin yan sandan, ya ce waɗanda ake zargin sun kai su 32, a cikin juragen ruwa 4 sun buɗe wuta ga jami’an yan sandan tunda suka yi ido huɗu da su.

A wannan batakashi da aka yi, huɗu daga cikin yan fashin sun rasa ransu, sauran kuma suka gudu a cikin jiragen ruwa uku.

Leave a Comment

%d bloggers like this: