Gwamnatin Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta tabbatar wa da BBC cewa ranar Lahadi, 7 ga watan Maris za a shirya muƙabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Kabara da malaman Jihar.

Kwamishinan Harkokin Addini Dr. Muhammad Tahar ne ya tabbatar wa da BBC saka ranar, inda ya ce za a gudanar da zaman da ƙarfe 9:00 na safiyar Lahadin.

“Ni a matsayina na kwamishina ni aka umarta da na kai wa Abduljabbar takarda, kuma na kai masa ita har gida, hannu da hannu har ma ya saka hannu na shaidar karɓa,” a cewar Muhammad Tahar.

Kwamishinan ya ce sauran malamai waɗanda suka rubuta takardar ƙorafi da murya ɗaya za su bayyana sunayen malaman da za su fafata da Abduljabbar zuwa ranar Laraba.

Ya ƙara da cewa Farfesa Sani Zahradden, Babban Limamin Kano, da Farfesa Shehu Ahmad Galadanchi, Babban Limamin Abuja, su ne za su jagoranci muƙabalar wato alƙalai.

Za a gudanar da muƙabalar ce a Fadar Sarkin Kano Aminu Ado Bayero.

Yanzu haka gwamnatin Kano na tsare da Abduljabbar Nasiru Kabara, inda ake yi masa ɗaurin talala a gidansa.

Gwamna Ganduje ya yarda a gudanar da taron muƙabalar ne biyo bayan kiran da Abduljabbar ya yi na cewa a yi masa adalci, a cewar sanarwar Muhammad Garba.

Tun a ranar 7 ga Fabarairu ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya amince a yi taron kuma aka faɗa wa ɓangarorin biyu su shirya fuskantar juna a tattaunawar ilimi.

Gwamnatin Kano ta zargi malamin ne da yin “kalaman tayar da fitina game da addinin Musulunci” bayan wasu malamai a jihar sun zarge shi da saɓa wa abin da Musulunci ya zo da shi.

Yadda za a gudanar da muƙabalar

Wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai Muhammad Garba ya fitar ranar 7 ga Fabarairu ta bayyana yadda muƙabalar za ta gudana.

“An bai wa waɗanda za su fafata a muhawarar mako biyu domin su tattara bayanai da maudu’an da za su tattauna a kai,” a cewar gwamnatin Kano.

An amince cewa dukkanin ƙungiyoyin addini za su turo wakilansu yayin muƙabalar, sannan za a gayyaci wasu manyan malamai daga wajen Kano domin su shaida.

Kazalika, Gwamna Ganduje ya yarda a yaɗa muhawarar kai-tsaye a gidajen rediyo na jihar da na ƙasashen waje.

Gwamnan ya yi kira ga mazauna jihar da su kwantar da hankali a lokaci da kuma bayan muƙabalar.

Leave a Comment

%d bloggers like this: