Kwamitin sauraron korafi na majalisar dattawa ta ce za ta binciki rawar da gwamnonin Neja-Delta su ka taka a wajen awon gaba da kudin NDDC.

A ranar Talata, 16 ga watan Maris, 2021, jaridar Punch ta rahoto majalisar dattawan ta na cewa binciken na ta zai iya kai wa ga gwamnonin yankin.

Ana zargin kowane daga cikin wadannan gwamnonin jihohi su tara sun karbi N100m daga hannun NDDC mai kula da cigaban yankin mai arzikin mai.

Rahoton ya ce kwamitin ya kuma ba shugaban rikon kwarya na NDDC, Effiong Akwa wa’adin sa’o’i 48 ya tattaro mata tsofaffin shugabannin hukumar.

Idan har Effiong Akwa bai iya kawo Daniel Pondei da ‘yan majalisar sa ba, majalisar dattawan ta yi barazanar za ta ba ‘yan sanda umarnin su cafke mata shi.

Ayo Akinyelure ya ce, “Mun riga mun duba yadda za a bada umarnin kama shi, mun yi 95% na aikin.”

“Mu na fito da barazanar kama shugaban rikon kwaryar, sai shugaban na NDDC ya zo ofishina, ya yi mani bayanin yadda aka batar da kudin da fatar-baki.”

“Su na ikirarin an ba kowane gwamna daga cikin gwamnonin Neja-Delta tara kudi Naira miliyan 100.”

Ya ce: “Sai mu ka ce su rubuta takarda, su yi wannan bayani kafin ranar 15 ga watan Maris, ranar Litinin kenan, amma har yau (Talata), ba mu ga komai ba.”

Sanata Ayo Akinyelure ya ce ba za a birne batun ba, ya ce dole majalisar dattawa ta binciki yadda aka batar da wannan kudin tallafin COVID-19 da NDDC ta bada.

Leave a Comment

%d bloggers like this: