Yan bindiga sun kashe karin mutanen Arewa takwas, yayin da aka ji wa wasu shida rauni a danyen hare-haren da su ka kai a jihar Imo a makon jiya.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa wannan hare-hare sun sa ‘Yan Arewa sun shiga cikin halin dar-dar da zaman firgici a jihar Kudu maso gabashin kasar.

A dalilin wannan mummunan lamari da ya ke auku wa, wasu mutanen da su ka fito daga Arewa sun fara kaura daga Imo, da-dama daga cikinsu sun koma gida.

Mun birne mutane takwas, sannan wasu mutane shida su na jinya a asibiti.” Inji Alhaji Iliyasu Sulaiman.

‘Dan kasuwan ya koka da cewa: “Ba mu san musababbin wannan abu ba, domin ba mu tsokano fada da kowa ba, amma su na ta kashe mutanenmu kamar hauka.”

A cewarsa, wannan kashe-kashe da ake yi ya tilasta wa fiye da mutane 100 sun bar Imo, sun koma inda su ka fito a cikin makonni biyun nan da su ka wuce.

Kawo yanzu na san mutane kusan 60 da su ka koma Sokoto, wasu fiye da 20 sun koma Kano da Katsina, sannan wasu su na shirin yin kaura.” Inji ‘dan kasuwar.

Alhaji Sani Ahmad Mai Rago ya ce baza jami’an tsaro a yankin Hausawa a Owerri kadai bai isa ba domin 30% na ‘Yan Arewa ne kadai su ke cikin aminci a yanzu.

Gwamnatin jihar Imo ta sha alwashin kare mutanen Arewan tare lallashinsu su zauna a garin. Wani hadimin gwamnan ya musanya cewa wasu su na barin gari.

Leave a Comment

%d bloggers like this: