Akalla mutane 10 ne rahotanni suka bayyana mutuwarsu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a kusa da garin Bara da ke cikin Karamar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi.

Kodayake bayanai kan abinda ya faru ba su da yawa, amma wakilin jaridar Punch ya samu labarin cewa hadarin ya faru ne da misalin karfe 7 na daren ranar Lahadi.

Rahotanni sun ce hatsarin ya faru ne lokacin da direban motar bas din da ke kan hanyarsa ta zuwa jihar Gombe daga jihar Kaduna ya yi kokarin kauce wa rami amma sai ya rasa gane kan motar ya fada daji.An ce daya daga cikin tayar motar ya fita kafin motar ta tarwatse.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa, reshen Jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da afkuwar hatsarin.

Abdullahi ya kara da cewa, “Da zaran aikin ceton ya kammala kuma na samu cikakkun bayanai game da hatsarin, zan tuntube ku dashi.”

Hakazalika, direban motar Toyota Hiace bas mai lamba BKD 265 XA ya mutu ranar Lahadi a wani hatsarin mota shi kadai a hanyar Zariya zuwa Kano.

Direban mai shekaru 40, mai suna Abdullahi Haruna, ya mutu ne a lokacin da ya isa asibitin Murtala Muhammed dake Kano, inda aka garzaya da shi.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi, a cikin wata sanarwa ya ce an mika gawar direban ga ofishin ‘yan sanda na ‘Yar Akwa bayan da likita ya tabbatar da mutuwarsa.

Wani Abdul Danlami Jibrin, na hanyar Zariya ya kira jami’an kashe gobara da misalin karfe 10:07 na safe don sanar da ita hatsarin; mutanen hukumar sun isa wurin da misalin karfe 10:19 na safe,” in ji sanarwar.

Leave a Comment

%d bloggers like this: