Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya, ASUU, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya da ta yi watsi da Tsarin Biyan Albashi na Bai Ɗaya, wato IPPIS, a matsayin sharaɗin da zai sa ta janye yajin aikinta.

Shugaban ƙungiyar ta ASUU na Ƙasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu tare da rabawa manema labarai a ranar Lahadi a Abuja, yana mai ƙarawa da cewa yajin aikin da suke yi zai iya ci gaba idan gwamnati ta gaza biya musu buƙatunsu.

Tun a cikin watan Maris ne ƙungiyar ASUU ta fara yajin aiki domin tilastawa gwamnatin tarayya biyan buƙatunta da suka haɗa da farfaɗo da jami’o’i, biyan alawus-alawus, sake tattauna yarjejeniyar 2009 da kuma kafa kwamitocin ziyara zuwa jami’o’i.

Mista Ogunyemi ya ce: “‘Yan Najeriya su yi mana haƙuri. ASUU suna yin gwagwarmayarsu ne.

“Ƙungiyarmu tana gwagwarmaya ne don tabbatar da cewa ‘ya’yan talakawa, waɗanda ba za su iya biyan kuɗaɗe masu tsada da ake biya ba a jami’o’in kuɗi ko kuma ba su da damar su yi karatu a wajen Najeriya sun samu ilimi mai inganci wanda ba zai gagare su ba.

“Wannan zai iya faruwa ne kawai idan gwamnati ta samar da isassun kuɗi ga jami’o’inta ta kuma ta yi maganin lalacewa da taɓarbarewar da suka yi.

“ASUU ta sauya matsayi a wasu abubuwa”, in ji Mista Ogunyemi.

 

Kakaki24

Leave a Comment

%d bloggers like this: