Shugabannin kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) na yankin kudu maso yamma sun umurci mambobinsu suyi kaura daga jihar Ebonyi sakamakon kashe-kashen da akayi kwanakin nan.

An zargi Fulani Makiyaya da laifin kisan mutane akalla 15 a karamar hukumar Ishielu ta jihar Ebonyi a makon da ya gabata.

Kungiyar Miyetti Allah idan mambobinta sukayi kaura na dan lokaci, za’a samu zaman lafiyan da zai bawa jami’an tsaro daman gudanar da bincike.

Shugabann Miyetti Allah na yankin, Gidado Siddiki, ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai ranar Laraba a Awka, babbar birnin jihar Anambara.

Siddiki yace, “Mun bada umurni dukkan makiyaya su fita daga jihar yanzu. Muna tsoron kada a kashesu da sunan ramuwar gayya. Shi yasa muka umurcesu su yi kaura daga jihar yanzu kuma su dawo idan abubuwa sukayi sauki.”

“Akwai takaici saboda Fulani Makiyaya sun yi shekara da shekaru a wajen kuma suna zaman lafiya da mutan garin.”

Siddiki ya yi kira ga Makiyaya dake yankin kada su dau doka a hannunsu.

Leave a Comment

%d bloggers like this: