Aliyu Mohammed, babban jami’in kwastam ya sanar da yadda suka baiwa ‘yan bindiga buhu 7 na shinkafa.

Aliyu Mohammed, shugaban sashi na 4 ta rundunar sintirin hadin guiwa a iyakokin kasar nan ta kwastam a arewa maso yamma, ya ce ya taba baiwa ‘yan bindiga buhu bakwai na shinkafa domin samun ‘yancinsa.

A yayin jawabi ga manema labarai a Katsina a ranar Talata, Mohammed ya ce lamarin ya auku ne a karamar hukumar Dutsinma ta jihar.

Mohammed yana tsokaci ne a kan kalubalen da jami’an hukumar kwastam ke fuskanta yayin sauke hakkin dake kansu, The Cable ta wallafa.

A yayin bada labarin karonsu da ‘yan bindiga a dajin Katsina, yace ‘yan bindigan sun bukaci buhu bakwai daga cikin buhuna 37 da muka kwace in har ana son a sako jami’ansu da rai.

Ya kara da yin bayanin cewa jami’ansu basu samun goyon baya cikakke daga jama’a.

Kamar yadda Mohammed yace, akwai wani lokaci da ‘yan sumogal suka tara ‘yan kauye da duwatsu suka dinga jifan jami’an kwastam.

A wani labari na daban, jihar Kano za ta karba kasonta na riga-kafin korona na AstraZeneca a ranar Talata. Tijjani Hussaini, shugaban kwamitin martani na jihar ya sanar da hakan a wata tattaunawa da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels a ranar Talata.

Leave a Comment

%d bloggers like this: