Sheikh Ibrahim Khalil, shugaban malaman arewa maso yamma yace darajar Abduljabbar bata kai a yi masa gangami ba

Shugaban malamai na arewa maso yamma, Sheikh Ibrahim Khalil, ya sanar da cewa kima da darajar Malam Abduljabbar Kabara basu kai ga malamai su yi masa gangamin taron dangi ba.

Sheikh Khalil ya sanar da hakan ne yayin tattaunawa da jaridar Leadership kan abinda ke faruwa tsakanin Abduljabbar da gwamnatin Kano.

Tun farko dai Ganduje ya haramtawa malamin yin wa’azi sakamakon zargin da da ake yi da bayar da wasu fatawoyi da suka sabawa koyarwar addini.

Malamin yace rashin darajar ne yasa Sarki Musulmi ya ki tura wakilan JNI wurin mukabalar.

 

Leave a Comment

%d bloggers like this: