Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bawa dukkan yan bindigan jiharsa wa’addin watanni biyu su tuba su mika makamansu

bawa dukkan yan bindiga da ke jiharsa wa’addin watanni biyu su tuba su mika makamansu idan kuma ba haka ba su fuskanci fushin hukuma, rahoton The Punch.

Da ya ke yi wa manema labarai jawabi a gidan gwamnati a ranar Talata, Gwamna Bello Matawalle ya ce gwamnati za ta yi maganin duk wani dan bindiga da ya ki mika wuya kafin wa’adin ya cika.

Ya kara da cewa nan ba da dadewa ba gwamnatin tarayya za ta aike da karrin sojoji 6000 zuwa jihar domin taimaka musu yaki da yan bindigan da suka yi saura.

“Na bak watanni biyu ku yi saranda ku mika makamanku sannan ku tuba kuma duk wani dan bindiga da bai rungumi zaman lafiya ba tabbas gwamnati za ta yi yaki da shi,” in ji gwamnan.

Ya yi kira ga dukkan kantomomin kananan hukumomi da masu rike da sarautun gargajiya su saka idanu a garuruwansu su kai rahoto idan an kai hari domin gwamnati ta dauki mataki.

Leave a Comment

%d bloggers like this: