Matashiyar mata mai shekaru 37 ta sheka lahira yayin da suke tsaka da lalata da saurayinta.

Wata mahaifiyar yara biyu mai suna Lugas ta rasa rayuwarta yayin da suke lalata da masoyinta, rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da hakan, The Nation ta ruwaito.

‘Yan sanda sun sake tabbatar da cewa sun damke saurayin mai suna Lekan Agboola domin su binciko asalin silar mutuwar matar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje, wanda ya zanta da manema labarai a garin Yola, ya ce an tsare Agboola a sashin binciken manyan laifuka na rundunar.

Agboola yace Lugas ta kasance budurwarsa na tsawon shekaru uku kuma yana da mata daya da ‘ya’ya biyu a Legas.

A yayin bayyana aukuwar lamarin, Agboola yace da kanshi ya kira marigayiya Lugas don ta same shi a gida.

Ya ce, “A ranar 24 ga watan Fabrairun 2021 wurin karfe 9 na safe. Na kira ta a waya inda na bukaci ta zo ta ganni domin na dade ban ganta ba. Tana zuwa muka fara shagalinmu amma babu dadewa ta fadi.

“A lokacin da na gane bata numfashi sai na kira wata kawata mace kuma na fada mata abinda ke faruwa. Ta shawarce ni da in mika ta asibiti inda aka tabbatar da ta mutu.”

Yan uwan marigayiyar sun zargi wata munakisa a labarin mutuwarta, hakan ne yasa suka bukaci rundunar ‘yan sanda da ta gano silar mutuwar ‘yar uwarsu.

Leave a Comment

%d bloggers like this: