An kama wani mutum da aka bayyana cewa malamin Islamiyya ne dan shekara 43, cikin mutane 34 da ‘yan sanda suka kwamushe a yammacin ranar Laraba kan laifin sace kayan mutane a kasuwar da iftila’in gobara ya rutsa da ita a Katsina.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa matar malamin Islmaiyyan ce ta kai shi kara wurin ‘yan sanda, bayan fuskantar cewa ya wawushe kayan jama’a kuma ya boye a karkashin gado.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce hakan ne ya kai ga kama mutumin mai suna Muhammad Abba.

Sauran mutanen da aka kama tare da malamin tare kananan yara ne da suka wawushe kayayyaki irinsu kayan sawa da na amfanin gida har ma da janereto da dai sauransu.

Yanzu haka dai suna fuskantar tuhuma a wajen ‘yan sandan jihar ta Katsina.

A ranar Litinin ne dai gobara ta tashi a babbar kasuwar Katsina ta yi kaca-kaca da shagunan cikin kasuwar, abin da ya kai ga tafka asarar dumbin dukiya masu darajar miliyoyin naira.

Leave a Comment

%d bloggers like this: