Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta cafke wata mata da ake zargi da hada kai da wasu mutum uku suka sace dan kishiyarta sannan suka lakada masa mugun duka har ya mutu.

Matar mai suna Christiana Wilson ta tabbatar da cewa ita da wasu mutum uku ne suka sace Edidiong Wilson mai shekaru 19 kuma suka kaishi daji tare da yi masa dukan kisa.

Kamar yadda Premium Times ta wallafa, bayan mutuwarsa, sun birne gawarsa a ranar 24 ga watan Disamban 2020, kamar yadda takardar ‘yan sandan ta nuna a ranar 26 ga watan Maris.

Ana zargin sun aikata laifin ne a Ikot Usekong dake karamar hukumar Eket ta jihar Akwa Ibom.

Sauran wadanda ake zargi da laifin sun hada da Saviour Peter, Richard Ekpenyong da Dominic Usoro.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Amiengheme Andrew, ya ce Wilson ta koma inda suka birne yaron bayan kwana shida inda ta hako gawarsa tare da cire kansa ta birne a wuri daban, inda tayi ikirarin cewa fatalwar yaron tana damunta.

Kamar yadda Wilson ta sanar da ‘yan sanda, ta dauka wannan matakin kan yaron ne saboda ya batar mata da wata N100,000 da ta bashi ajiya.

Leave a Comment

%d bloggers like this: