Wata matar aure, mai suna Marwanatu Muhammad a ranar Litinin ta roki kotun Shari’a da ke zamanta a Rigasa Kaduna, ta raba aurenta da mijinta Iliyasu kan cewa ya gaza yi mata ciki, The Nation ta ruwaito.

A karar da ta shigar, Marwanatu, ta yi ikirarin cewa Iliyasu ya gaza yi mata ciki tunda suka yi aure shekaru 10 da suka shude a 2011.

“Ya taba yin aure a baya amma matarsa ta rabu da shi saboda baya haihuwa. Ina tunanin nawa zai banbanta amma ashe kuskure na yi,
“Lafiya ta kalau ba ni da matsala. Bana ra’ayin cigaba da zaman auren. A shirye na ke in mayar masa kudin sadakinsa, N20,000,” in ji ta.

A bangarensa, Iliyasu ya ce yana bin wacce ta yi karar bashin N17,000 kuma yana son kotu ta taimaka ta karbo masa bashin.

Tunda farko, Alkalin kotun Mallam Salisu Abubakar-Tureta ya umurci ma’auratan biyu su tafi asibiti a musu gwaji domin gano inda matsalar ya ke.

Leave a Comment

%d bloggers like this: