A ranar Alhamis ne masu garkuwa da mutane suka dawo kan babbar hanyar Abduja zuwa Kaduna, inda ake zargin suna ci gaba da garkuwa da matafiya da ba a san yawansu ba.

An samu sauƙin yin garkuwa da matafiya a babbar hanyar tun lokacin da aka hana tafiye-tafiye tsakanin jihohi sakamakon ɓarkewar annobar COVID-19 a ƙasar nan.

Shaidu sun shaida wa Daily Nigerian cewa harin ya afku ne a kusa da ƙauyen Katari da misalin ƙarfe 9:00 na safe.

Mohammed Lawan, wanda ya tsira daga harin, ya faɗa wa Daily Nigerian cewa masu garkuwa da mutanen sun kai wa matafiya masu zuwa Kaduna hari da misalin ƙarfe 8:50 na safe.

“Bai wuce mita 250 kafin mu ƙarasa wajen ba a sai muka tsaya da muka hango su. Na hango Honda CRV 98 Model ƙofofinta a buɗe ba kowa a ciki, alamar da ke nuna cewa sun yi garkuwa da waɗanda suke ciki.

“Daga nan sai muka ji ƙarar bindigu a lokacin da helikwafta ya dira ya mamaye wajen”, in ji Mista Lawan.

Har yanzu ‘yan sanda ba su mayar da martani a kan wannan al’amari ba.

Leave a Comment

%d bloggers like this: