Yayinda ake gab da shiga watan Ramadana.An kaddamar da rabon buhuhunan shinkafa da kayan hatsi na tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a jihar Kano.

A hotuna da bidiyoyi da suka bazu a kafafen ra’ayi da sada zumunta, an ga mutane da buhuhunan shinkafa mai rubutun ‘JAGABA – Asiwaju Bola Ahmed Tinubu’ ana raba musu.

Wata mai suna @mansurah_isah a shafin Instagram ta daura hotunan inda take godiya ga gidauniyar Tinubu kan wannan kayan abinci.

Wannan abu ya biyo bayan rade-radin cewa Tinubu na shirin takaran kujeran shugaban kasa a 2023.

Leave a Comment

%d bloggers like this: