Tsohon Sanata, Dino Melaye ya roki Shugaba Muhammadu Buhari ya mika mulki ga Mataimakinsa, Yemi Osinbajo yayin da yake shrin tafiya zuwa Landan don duba lafiyarsa, PM News ta ruwaito.

Fadar Shugaban kasa ta sanar a ranar Litinin cewa Buhari zai yi tafiya zuwa Landan ta kasar Ingila don duba lafiyarsa kuma zai dawo nan da makonni biyu.

Don haka Dino Melaye, a cikin wani sakon Twitter ya ce ya kamata Buhari ya mika mulki ga Mataimakin Shugaban kasa ta hanyar rubuta wasika zuwa ga Majalisar Dokoki ta Kasa.

Ya bukaci cewa shugaban ya yi hakan kafin barin kasar a ranar Talata.

Leave a Comment

%d bloggers like this: