Rahotanni sun bayyana cewa wani daga cikin masu ba gwamnan jihar Katsina shawara, Rt Hon Aminu Bello Masari, ya fadi a wurin bikin aure.

Jaridar Katsina Post ta fitar da rahoto cewa daga wannan yanke jiki ne Alhaji Rabe Ibrahim Jibia ya rasu a ranar Asabar, 27 ga watan Maris, 2021.

Marigayi Rabe Ibrahim Jibia shi ne mai ba mai girma gwamnan jihar Katsina shawara a kan harkar tsaron na abin da ya shafi shiyyar garin Daura.

Wannan Bawan Allah ya fadi ne a lokacin da ake daura auren ‘diyar wani abokin aikinsa, Alhaji Ibrahim Katsina a unguwar GRA, Katsina.

Shi ma mahaifiyar wannan Amarya, Alhaji Ibrahim Katsina ya na cikin masu ba gwamna Aminu Bello Masari shawara a kan sha’anin tsaro.

Ba a dade da gwamnan Katsina ya nada Rabe Ibrahim Jibia a matsayin mai ba shi shawara ba, sai rai ya yi halinsa, shi kuwa ya ce ga garinku nan.

Da aka ruga da Marigayi Rabe Ibrahim Jibia zuwa asibitin gidan gwamnati bayan ya yanke jiki, sai likitoci su ka tabbatar da cewa ya riga ya cika.

Jaridar ta ce marigayin tsohon jami’in hukumar DSS masu tsaro ne leken asiri da fararen kaya ne bayan ya yi ritaya ne aka ba shi mukami a gida.

Tuni aka yi masa sallar jana’iza, aka bizne, shi a garin Katsina kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Leave a Comment

%d bloggers like this: