Wani ƙwararre a fannin rayuwar tsuntsaye, ya dauki hoton wani tsuntsu a jihar Pennsyvania da aka bayyana cewa mata-maza ne.

Mai dabi’ar bin diddigi da kuma kallon tsuntsayen, ya garzaya da na’urar daukar hotonsa bayan da ya ji cewa wani abokinsa ya ga tsuntsun wanda ake yi wa laƙabi da suna ‘northern cardinal’.

Duk da cewa ba wai ba a taba jin labarin ba, amma kuma ba kasafai ake samun tsuntsaye mata-maza ba.

Launin namijin tsuntun na ‘cardinal’ ja ne, yayin da matan kuma launinsu kasa-kasa ne, da hakan ya nuna cewa wannan ka iya zama gamin gambizar duka biyun ne.

Kwararre fannin rayuwar tsuntsaye Jamie Hill, mai shekaru 69, ya shaida wa BBC cewa akan samu irin wannan “amma bai wuce sau daya cikin miliyan ba.”

Abokiyar Mista Hill ta shaida masa cewa ta taba ganin “tsuntun da ba a saba gani ba” yana shiga cikin wurin cin abincin tsuntsayenta a karamar hukumar Warren a jihar Pennsylvania.

Da farko Mista Hill na ganin ko tsuntsun ko yana da wata tawaya ta rashin launi ce a gashinsa, amma kuma ba zai kasance rabi namiji rabi mace ba.

Amma bayan kallon hotunan da aka dauka da wayar salula, ya yi tunanin ko yana da abin da a kimiyyance ake kira ‘bilateral gynandromorphism’, wanda ke faruwa idan tsuntsu ya samu duka ƙwayoyin haihuwa masu aiki da kuma ƙwayar mazakuta daya mai aiki a lokaci guda.

Ya ziyarci gidan da aka ga wannan tsuntsu mai nau’in ‘cardinal; A cikin sa’a daya ya samu ya dauki hoton tsuntsun na ba kasafai ba.

“Bayan da na dauki hotunan, zuciyata na bugun dai-dai a cikin sa’oi biyar har sai na isa gida domin in duba hotunan da kyau don ganin ainihin abin da nake da shi,” Mr Hill ya bayyana.

“Na shafe kusan shekaru 20 ina neman nau’in tsutsun nan na woodpecker mai bakin ƙaho da aka dade ana tunanin ɓacewarsa daga doron kasa, kuma daukar hoton wannan da ba a saba gani ba, abu ne mai matukar muhimmanci da nake tunani ka iya sa in gano tsuntsun na ‘woodpecker’,” ya ce.

a cika samun tsuntsaye mata-maza ba, in ji farfesa Brian Peer a Jami’ar Western Illinois, wanda ya gudanar da bincike kan irin na’uin tsuntsu na ‘bilateral gynandromorph northern cardinals’ a Amurka.

Amma ya kara da cewa, irin wannan ka iya kasancewa ba tare da an gane ba a tsakanin wasu halittun.

Northern cardinal

“A bayyane take cewa yanayin halittar ‘Bilateral gyndromorphism’ na faruwa a bisa kuskuren rarrabuwar kwayoyin halitta,” in ji shi.

“Ƙwai da abubuwan da ke kewaye da na kyankyasa daga maniyyi da ban. Sakamakon na kasancewa halittar mace da namiji.”

Wannan nau’in tsuntsu na ‘gynandromorph northern cardinal’ ba shi ne na farko da aka fara gani ba a yankin.

A shekarar 2019 an ga wasu tsuntsayen irin wannan, kamar yadda hukumar nazari kan kimiyyar kasa ta bayyana.

Mr Hill ya yi hasashen cewa tsuntsun cardinal din da ya gani ka iya kasancewa irin wancan ɗin ne.

Farfesa Peer ya jaddada cewa tsuntsayen ‘northern cardinals’ an sama ganinsu a Arewacin Amurka.

Saboda mace da namiji na da bambanci sosai wajen kamanni, da hakan ke saukakawa wajen gano nau’in tsuntsu ‘gynandromorph’.

Leave a Comment

%d bloggers like this: