Allah ya yiwa mahaifin daya daga cikin daliban jihar Kaduna da aka sace ya rasu

Gwamnatin jihar Kaduna ta gana da iyayen yaran kan halin da ake ciki. Makonni biyu kenan da sace daliban makarantar Afaka babu labari

Mahaifin daya daga cikin daliban makarantar FCFM Afaka 39 da yan bindigan suka sace a jihar Kaduna, Ibrahim Shamaki, ya mutu.

Channels TV ta rahoto cewa Ibrahim, mahaifi ne ga Fatima Shamaki, daya daga cikin dalibai matan da suka bayyana a bidiyon da yan bindigan suka saki.

A cewar majiya daga iyalan mamacin, Ibrahim Shamaki ya mutu sakamakon bugun zuciya bayan rashin lafiyan da ya fada bayan samun labarin sace diyarsa.

Ya mutu da yammacin Juma’a yayinda yan’uwansa ke kokarin kai shi asibiti.

Labarin mutuwar Ibrahim na zuwa ne bayan gwamnatin jihar ta zanna da wakilan iyayen daliban a gidan gwamnatin jihar.

Yau makonni biyu kenan da sace daliban.

Leave a Comment

%d bloggers like this: