Yan Najeriya sun kwararawa wata budurwa sakonnin taya murna ga kyakkyawar budurwa yar Arewa bisa nasaran da ta samu.

Budurwar mai suna Maryam Musa ta yi sanarwa a shafin Tuwita bisa kammala karatun digirinta a fannin karatun lauya.

Maryam, wacce bata bayyana jami’ar da ta kammala ba ta godewa Allah bisa nasarar da ta samu.

Yan Najeriya sun jinjina mata bisa irin kyawun da Allah ya bata yayinda wasu ke taya ta murnan kammala karatunta.

Hakazalika wasu sun bata shawari kan rayuwa bayan karatu.

Wasu daga cikin mabiyanta a twitter sun bayyana ra,ayinsu kamar haka:
@AliyuIbrahimA13 yace: “Ina tayaki murna Barista. ina bukatar kyakkyawar lauya irinki, wacce za ta iya rikita Alkali.”

@Mushin24789 yace; “Ki kasance mai gaskiya duk inda kika samu kanki kuma kada kiyi rashin adalci a aiki…”

@Omacares1 yace: “Allah ya cigaba da kare ki da shiryar dake hanya madaidaici bisa wannan babban nasara.”

Leave a Comment

%d bloggers like this: