Wasu yan mata uku sun bayyana cewa suna soyayya da saurayi daya da duk suka hadu da shi a shafin Twitter.

– Shafin Twitter mai suna @KevinEmmilie4 ta wallafa hotunanta da saurayinta, sannan wasu mata biyu suka wallafa nasu hotunan don tabbatar da cewar mutum dayua suke soyayya da shi

– Mabiya kafar sadarwar sun yi sharhi cike da mamakin abunda idonsu ya gane masu

An fallasa wani mutumi da ya hadu da kuma fara soyayya da mata uku a shafin Twitter bayan daya daga cikin matan ta yi jinjina gare shi a dandalin sada zumunta.

Lamarin ya fara ne lokacin da @KevinEmmilie4 ta wallafa hotunanta da na saurayinta sannan ta rubuta:

“A Twitter muka hadu.”

Da take martani ga lamarin, wata budurwa mai suna @sharon_kiwanuka a Twitter ta ce itama ta hadu da matashin a Twitter, Ba da jimawa ba, sai budurwa ta uku a hoton ta fito da nata hujjar don nuna cewa ita ma ta hadu da mutumin a Twitter.Tuni mabiya shafin @sharon_kiwanuka suka yi tururuwan sharhi masu ban dariya.
“Amma ga dukkan alamu yana farin ciki sannan kuma kuna farin ciki das hi, don haka ban wani matsala ba a nan.”

Leave a Comment

%d bloggers like this: