Sunday Adeyemo, wani dan gwagwarmayar Yarbawa wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya fada wa gwamnatin tarayya da ta cire shi daga cikin jerin gwanon da take yi sannan ta bi shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau da ‘yan fashi.

Igboho ya yi wannan furucin ne a ranar Juma’a 26 ga Fabrairu, bayan da aka dakile kama shi da jami’an tsaro suka yi yunkurin yi.

An rawaito cewa jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya da kuma jami’an tsaron farin kaya (DSS) sun tsare motar dan fafutukan a hanyar babban titin Lagas-Ibadan.

An tattaro cewa dan fafutukan Yarbawan na kan “hanyarsa ta ganin Baba Ayo Adebanjo”, wani dattijo yarbawa kuma daya daga cikin shugabannin Afenifere a Legas.

Igboho wanda ya yi magana a wani faifan bidiyo wanda yanzu ya fara yaduwa ya ce ya koma gidansa da ke Ibadan.

“Ku je ku sa su gayyato Gumi da Shekau tukuna kafin su dame ni. A bar su su fuskanci ‘yan fashin maimakon haka,” kamar yadda ya fada wa jaridar The Punch bayan artabun da suka yi da jami’an tsaro.

 

Leave a Comment

%d bloggers like this: