Kotun da ke zama a Ikot Ekpene ta samu samu Farfesan ne da sauya sakamakon zaben kananan hukumomi guda biyu da suka hada da Oruk Anam da Etim Ekpo domin taimakawa ‘dan takarar Jam’iyyar APC kuma tsohon Gwamnan Jihar Godswill Akpabio a zaben shekarar 2019.

Sahihan alkaluman da aka tattara sun nuna cewar Chris Ekpenyong, dan takarar Jam’iyyar PDP ya samu nasarar lashe kujerar, abinda ya sa aka gurfanar da Farfesa Ogban a gaban kotu. Masu sanya ido kan harkokin zabe a Nijeriya sun dade suna cewa rashin hukunta malaman zabe na daga cikin matsalolin da suka addabi zaben a kasar nan.

Leave a Comment

%d bloggers like this: