Jaridar The Nation ta ce babban kotun tarayya da ke garin Ilorin, jihar Kwara, ya hana gwamnatin jihar Kwara damar karbe gidan Ile-Arugbo.

Alkalin kotun ya kuma haramta wa gwamnatin Kwata karbe wasu filaye uku da Marigayi Dr. Olusola Saraki ya mallaka a lokacin rayuwarsa.

An samu babban kotun da ta yi fatali da karar da Asa Investment Ltd ya shigar, ya na neman a hana gwamnatin Kwara karbe wadannan filayen

Rahotanni sun bayyana cewa tuni gwamnatin AbdulRazaq AbdulRahman ta fara gine-gine a kan wadannan filayen da ake ta rikici a kansu a kotu.

A shari’a mai lamba KWS/112/2021, kamfanin Asa Investment da wani mutum sun kai karar gwamnatin jihar Kwara da majalisar dokokin jihar.

Alhaji AbdulRazaq AbdulRahman, kwamishinan shari’a, Darektan hukumar sifayo, shugaban ‘yan sanda na kasa su na cikin wadanda aka hada a karar.

An bukaci gwamnati ta dakatar da karbe wadannan kadarori da marigayin ya bar gado, ko a bada kyautarsu, ko kuma a fara yin wani gine-gine a kansu.

Wadanda su ka shigar da kara a kan wadannan filaye da ke kan titin Ilofa a unguwar Ilorin GRA, sun nemi ka da a taba fulotan har sai an gama sharia’a.

Alkali mai shari’a, Adenike Akinpelu, ya amince da rokon da aka gabatar, ya bada umarni ka da wadannan filaye har zuwa lokacin da aka karkare karar.

A zaman da aka yi a ranar Talata, kotu da dakatar da sauraron karar sai 19 ga watan Afrilu, 2021.

A bara kun ji cewa har sai da ta kai fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta shiga rikicin da ake yi a Kwara tsakanin gidan Saraki da gwamna mai-ci.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnan Kwara ya ruguza wani tsohon gida na Olusola Saraki, mahaifin Dr. Abubakar Bukola Saraki da Gbemisola Saraki.

Leave a Comment

%d bloggers like this: