Hukumar NCDC ta ruwaito cewa, mutane 48 ne kadai suka kamu da cutar ta Korona daga jihohi 8 a ranar Litinin, wata alama kuma da ke nuna cewa mai yiwuwa kwayar cutar na neman fita daga Nijeriya, PM News ta ruwaito.

Sabanin haka an bada rahoton kamuwar mutane sama 104 a ranar Lahadi.

Daga cikin sabbin wadanda suka kamu 48, Legas tana da 13 sai kuma Kaduna mai mutum 7.

Har ila yau, Nasarawa ta bayar da rahoton kamuwar mutane bakwai, Kano 6, Kwara 5, Ondo 4, Akwa Ibom 3 sai kuma Osun 3.

Ya zuwa yanzu, an tabbatar da wadanda suka kamu da cutar sun kai 162,641, daga cikin samfura 1,767,694 da aka gwada.

Adadin wadanda aka sallamar ya kai 150,466, yayin da wadanda har yanzu suke killace suka kai kimanin 10, 126.

An bada rahoton mutuwar mutum daya tak, a rahoton na ranar Litinin, sabanin bakwai a ranar Lahadi.

A cewar NCDC, adadin wadanda suka mutu yanzu ya kai 2,049.

Leave a Comment

%d bloggers like this: