Mahaifin matar da kishiyarta hallaka ta hanyar banka mata wuta ya bukaci hukumomi su tabbatar da cewa an kashe wacce aka kama da wannan laifi.

Malam Ibrahim Yayaha Sidi Na Khalifa ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da Daily Trust.

Ya ce abinda yake so kawai shine a yanke mata hukuncin da ya kamata.

Ya ce a addinin Musulunci, babu laifi idan mutumin da aka zalunta ya zabi daukar fansa saboda Al-Qur’ani ya bayyana hukuncin kisa ba tare da hakki ba.

“Ba zan taba yafe jinin diyata ba. Qur’an yace ‘ Mun hukunta cewa rai ga rai’…. saboda haka ina son ganin an yanke hukunci kan wadanda suka aikata wannan abin takaicin,” Yace.

“Ba zan taba yafe musu ba. Ba hadari bane ko kuskure. Ki bugi diyata har lahira, sannan ki bankawa gawarta wuta, ba zan taba yafewa ba.”

1 Comment

  • Posted March 27, 2021 4:20 pm 0Likes
    Bashir muhammmad

    Bashir

Leave a Comment

%d bloggers like this: