Fitaccen dan kwallon kafar Argentina Lionel Messi, mai shekara 33, ya shirya sabunta kwangilarsa a Barcelona bayan zaben sabon shugaba Joan Laporta, a cewar tsohon dan wasan Barca Rivaldo. (The Sun)

Arsenal ba ta da damar sayen dan wasan da ta karbo aro daga Real Madrid Martin Odegaard, mai shekara 22, yayin da kungiyar ta Sifaniya take kallon dan wasan a matsayin wanda za ta ci moriyarsa nan gaba. (Marca – in Spanish)

Dan wasan Liverpool dan kasar Netherlands Georginio Wijnaldum, mai shekara 30, na bukatar dakatawa har sai Barcelona ta sayar da dan wasan Bosnia Miralem Pjanic, mai shekara 30, kafin ya kammala shirinsa na tafiya Nou Camp. (Sport via Mirror)

Kazalika kocin Ronald Koeman yana son daukar dan wasan Inter Milan da Belgium Romelu Lukaku, 27. (Calcio Mercato)

Liverpool na kan gaba a tsakanin kungiyoyin da ke son daukar dan wasan PSV Eindhoven Donyell Malen, duk da cewa kungiyoyi irinsu Juventus da AC Milan suna zawarcin dan wasan na Netherlands mai shekara 22. (Gazzetta Dello Sport via Goal)

Za a sabunta kwangilar Ole Gunnar Solskjaer, mai shekara 48, ko da kuwa Manchester United ta kammala kakar wasa ta bana ba tare da daukar Kofi ba.

Mutumin da ya mallaki Sheffield United Yarima Abdullah ya ce ba ya son korar kocin kungiyar Chris Wilder daga aiki kuma ya yi ikirarin cewa tsohon kocin kungiyar ya bukaci a ba shi £4m domin ya ajiye aiki. (Sky Sports)

Dan wasan Najeriya Kelechi Iheanacho, mai shekara 24, yana shirin sabunta kwangilarsa a Leicester City a bazarar nan. (The Sun)

Barcelona na son daukar dan wasan Eintracht Frankfurt dan kasar Portugal mai shekara 25 Andre Silva. (Marca)

Babu tabbas game da makomar Zinedine Zidane a Real Madrid bayan kakar wasa ta bana, a yayin da French Football Federation ke son daukarsa. Kwangilar kocin dan kasar Faransa mai shekara 48 ba za ta kare a Madrid ba sai 2022. (AS)

Masar ta ce tana son Mohamed Salah ya kasance cikin tawagarta da za ta buga gasar Olympic a bazarar nan, inda hakan ke nufin ba zai buga wasannin da Liverpool za ta yi ba gabanin soma kakar wasa mai zuwa.

Leave a Comment

%d bloggers like this: