Hare-haren makiyaya na baya-bayan nan a fadin yankin Igbo ya haifar da tashin hankali a yankin kudu maso gabas

Ndinne Igbo, wata kungiyar zamantakewar mata, ta yi barazanar cewa mambobinta za su yi tattaki tsirara a fadin kasar ta Igbo don nuna rashin amincewa da kashe-kashen da makiyaya ke yi a yankin idan har hukumomin da abin ya shafa ba su shawo kan lamarin ba.

Yankin kudu maso gabas na fama da rikice-rikicen makiyaya a makwannin da suka gabata, wanda yayi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane.

Kungiyar ta yi Allah-wadai da harin makiyaya da ya auku a jihohin Enugu da Ebonyi, inda ta koka kan yadda yara ‘yan kabilar Ibo da dama suka zama cikin mummunan harin.
Kungiyar a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jagoran ta, Misis Beatrice Chukwubuike, a ranar Asabar, 3 ga Afrilu kuma Legit.ng ta gani, ta yi kira ga shugabannin Najeriya da na Ibo da su kamo wannan mummunan lamarin kafin ya tabarbare.

Leave a Comment

%d bloggers like this: