Shugaban hukumar da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa a jihar wato KAROTA, Dakta Baffa Babba Dan’agundi ya bayyana cewa hukumar ta sa za ta tarawa jihar Kano haraji na naira biliyan Ɗaya da miliyan 500 a cikin shekara mai kamawa ta 2021.

Dakta Bappa Babba Ɗan-Agundi ya bayyana haka ne a lokacin da yake kare kasafin kuɗin hukumar a zauren Majalisar Dokokin Jihar Kano a yau Litinin.

Shugaban KAROTAR ya ƙara da cewa Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya baiwa hukumar damar ɗaukar sabbin ma’aikata har 1,400.

Ya ce a halin da ake ciki, hukumar KAROTA ta ɗauki ma’aikata 700, zuwa Janairu, 2021 kuma za su ƙara ɗaukar wasu sabbin ma’aikatan 700.

A ƙarshe shugaban na KAROTA ya ce hukumarsa za ta haɗa kai da Hukumar Gyara Tituna ta Jihar Kano, KARMA, domin ganin sun tsaftace jihar.

 

Kakaki24

Leave a Comment

%d bloggers like this: