Jirgin yaki na sojin saman Najeriya dake ayyukan yau da kullum a yankin arewacin Najeriya ya bace.

Wannan yana kunshe ne a wata wallafa da kakakin rundunar sojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gabkweet yayi a shafinsa na Twitter kuma Legit.ng ta gani a daren Laraba, 31 ga watan Maris.

Ya wallafa: “Wani jirgin NAF dake ayyukan yau da kullum na taimakawa dakarun sojin kasa a yankin arewacin Najeriya ya bace. Ana kokarin ganin an gano inda yake. Karin bayani na nan tafe.”

Leave a Comment

%d bloggers like this: