Hukumar dake da alhakin shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire JAMB ta fitar da jadawalin yadda jarabawar share fagen shiga jami’a UTME na bana zai kasance.

Kamar yadda hukumar JAMB ta fitar, za’a yi jarabawar UTME daga ranar Asabar 5 ga watan Yuni zuwa Asabar 19 ga watan na Yuni.

Hukumar ta kuma bayyana cewa za’a fara rijistar neman izinin zana jarabawar ta bana daga ranar Alhamis takwas ga watan Afirilu zuwa ranar Asabar 15 ga watan Mayu.

Haka zalika, hukumar JAMB ta ce babu wani ƙarin lokaci da zata yi na siyar da fom din UTME ko kuma na DE.

Hukumar ta fitar da wannan sanarwar ta hannun shugabanta dake kula da bangaren yaɗa labarai, Dr Fabian Benjamin, a yau Laraba.

Sanarwar ta bayyana cewa dole ɗuk wani ɗalibi ya tanaji lambar katin zama ɗan kasa wato NIN kafin ya yi rijista, jaridar The Nation ta ruwaito.

JAMB ta ƙara da cewa amfani da lambar katin zama ɗan ƙasa NIN wajibi ne ga duk wanda keson zana jarabawar bana 2021.

Ta kuma bayyana cewa za’a yi rijistar jarabawar a cibiyoyin zana jarabawar 700 dake faɗin ƙasar nan.

 

Leave a Comment

%d bloggers like this: