Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi waiwaye kan yakin basasan da aka kwashe watanni 30 ana yi a Najeriya kuma ya yi addu’a kada Allah ya maimaitawa Najeriya irin wannan yaki.

Mai magana da yawun shugaban kasan, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya sake mai taken “Shugaba Buhari ya aika ta’ziyya ga shahidan yakin basasan Najeriya.”

Najeriya, karkashin Janar Yakubu Gowon ta shiga yaki da Biyafara da suka balle karkashin jagorancin Laftanar Kanar Odumegwu Ojukwu tsakanin 6 ga Yulin 1967 da 15 ga Junairun 1970.

Shehu ya ce Buhari ya yi waiwayen ne lokacin da ya karbi bakuncin shugaban mazhabar Tijjaniyya, Sheikh Muhammadul Mahy Niass.

“Buhari ya ce a watanni 30 da akayi yakin basasa, an yi rashin rayukan yan Najeriya kuma ya yi addu’an kada mu sake ganin irin wannan yaki.”

A cewar Garba Shehu, Buhari ya yi maraba ga Khalifan kuma ya jinjinawa kokarin da sukeyi wajen kawo karshen matsalar tsaron da kasar ke fuskanta.

Leave a Comment

%d bloggers like this: