Ƙungiyar malaman jami’o’in ta ƙasa ASUU ta yi watsi da rahoton cewa ta janye daga yajin aiki ta ke kan yi.

Shugaban kungiyar ta ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemii, ne ya bayyana haka a jiya Asabar, inda ya ce har yanzu yajin aikin watanni takwas da su ke yi ya na nan daram dam.

Tun da farko Farfesa Biodun Ogunyemi ya karyata rahoton cewa ASUU ta janye daga yajin aiki kuma ya jaddada cewa ASUU ba ta da shafin Tuwita.

“Ƙungiyar ASUU ba ta da shafi a Tuwta. Mutane da dama suna damu na da kiraye-kirayen waya kuma na gaji”

Kungiyar ta ASUU ta fara yajin aikin ne tun a cikin watan Maris gabanin bullar cutar Korona a Najeriya.

Daliban Najeriya dai da iyayensu da sauran ma su ruwa da tsaki sun kosa da ganin an warware matsalolin da su ka dabaibaye lamarin jami’o’in kasar nan ko za a samu su cigaba da karatunsu kamar yadda yayan manyan jami’an gwamnati da na masu hannu da shuni su ke yi a jami’o’i masu zaman kansu ko ma na kasashen waje.

Leave a Comment

%d bloggers like this: