Gwamnatin Kano ta rushe inda Malam Abduljabbar Nasir Kabara ke bayar karatu kusa da Jauful Fara, da ke filin mushe.

An ɗauki lokaci ana rikici kan filin tsakanin malamin da mutane a unguwar ta filin mushe da Mallam Abduljabbar ke karatu.

Gwamnati ta ƙwace filin sakamakon koke da ta samu daga mutanen yankin, kan cewar filin mallakinsu ne.

Kimanin wata biyu kenan gwamnati ta fitar da filaye a wajen ciki har da na Malam Abduljabbar da ya yi iƙirarin gwamnatin da ta shuɗe ce ta ba shi.

Leave a Comment

%d bloggers like this: