Gwamnatin jihar Kano ta karyata batun rushe ginin makarantar Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da ke birnin jihar.

Kakakin hukumar tsara muhalli ta jihar Kano wato KANUPDA, Ado Muhammad Gama, ya sanar da sashin Hausa na BBC cewa gine-ginen da aka rusa suna kusa da wajen da malamin ke bayar da karatu amma ba nasa ba ne,
Ya ce:

“Su gine-ginen da ake magana a kai, wasu mutane ne suka yi su ba bisa ka’ida ba shi ya sa yanzu muka rusa su.

Tunda farko dai An bukaci mutanen da suka yi ginin a kan kada su soma shi amma sai suka yi burus da batun shi ya sa aka rusa fine ginen masu.

Ya kuma tabbatar da cewar makarantar Sheikh Abduljabbar tana nan babu abin da ya same ta.

Leave a Comment

%d bloggers like this: