Tun farko, wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro Samuel Aruwan ya fitar ta ce sojoji sun yi nasarar kuɓutar da ɗalibai da yawa kafin ‘yan bindigar su gudu da su.

“Sojojin Najeriyar sun samu nasarar ceto mutanen 180; dalibai mata 42, da malamai takwas da kuma dalibai maza 130.

Amma kuma har yanzu ba a gano sauran dalibai maza da mata kusan 30 ba”, in ji Aruwan.

Kawo yanzu kusan ɗalibai 800 aka sace tun watan Disamba kuma wannan ne karo na uku da aka sace ɗalibai daga makarantunsu a shekarar 2021 a Najeriya.

A jihar Kaduna kaɗai, ‘yan bindiga sun kashe mutum 937 sannan suka yi garkuwa da 1,972 a shekarar 2020.

Sanarwar ta kuma cewa dakarun soji ne suka kai dauki cikin makarantar, inda suka fafata da ‘yan bindigar.

Wasu daga cikin daliban da aka ceto sun samu raunuka, kuma ana duba lafiyarsu a wani asibitiin sojoji na Kaduna, a cewar sanarwar.

Leave a Comment

%d bloggers like this: