Bayan mako guda, gwamnatin Kwara ta sanar da matsayarta kan lamarin sanya Hijabi.

Gwamnatin jihar Kwara ta bada umurni ga dukkan makarantun gwamnati da makarantun da mabiya addinin Kirista suka assasa cewa kada wanda ya hana dalibai mata sanya Hijabi.

Hakazalika ya bada umurnin bude makarantu 10 da aka rufe makon da ya gabata.

Wannan na kunshe cikin jawabin da Sakataren gwamnatin jihar, Mamma Jibril ya saki ranar Alhamis.

A zaman da bangarorin Musulmai da Kirista sukayi da jami’an gwamnatin jihar, dukkansu sun ki janyewa daga matsayarsu.

Yayinda Musulmai suka tsaya kan bakansu cewa lallai sai an bar dalibai mata su sanya hijabi saboda dokar kasa ta amince da haka, Kiristoci sun ce sam basu yarda ba saboda ya kamata ayi la’akari da manufar kafa makarantun.

Amma gwamnatin jihar a hukuncin da ta yanke, ta ce ta yi kyakkyawan dubi ciki dukkan lamuran kuma ta yanke shawara.

Yace: “Saboda haka, gwamnati ta tabbatar da cewa daliba Musulma na da hakkin sanya hijabi a makaranta, kuma ta umurci ma’aikatar Ilimi da ta fitar da samfurin Hijabin da za’ayi amfani da shi a dukkan makarantun gwamnati da na Mission.”

“Duk dalibar da take da niyyar sanya Hijabi a makarantu na da hakkin yin hakan.”

Leave a Comment

%d bloggers like this: