Kwamishinan lafiya na jihar Legas Farfesa Akin Abayomi ya sanar da sakamakon gwaji ya tabbatar da Sanwo-Olu ya na dauke da COVID-19.

Abayomi, wanda ya sanar da hakan ta shafinsa na Twitter@ProfAkinAbayomi a daren jiya asabar, yana mai fatan samun lafiya ga gwamnan na jihar Legas nan ba da jimawa ba.

Ya ce gwamnan na karba kulawar kuma yana cikin hayyacisa wanda akesa ran zai samu lafiya nan ba da jimawa ba.

Ya kuma bukaci al’ummar jihar Legas dasu dukufa wajan yin addu’a ga gwamnan domin ya sami lafiya ya dawo bakin aikinsa.

Leave a Comment

%d bloggers like this: