Muhammad Matawalle, ta bada umurnin rufe dukkan makarantun kwana dake jihar gaba daya, rahoton TVC.

Matawalle ya yi hakan sakamakon sace daliban makarantar sakandaren GGSS Jangebe da aka sace a karamar hukumar Talata Mafara dake jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da yammacin Juma’a a Gusau, birnin jihar.

Matawalle ya jaddada cewa zai cigaba da shirin yin afuwa ga yan bindiga domin su ajiye makamansu.

A cewarsa, harsashi ko da guda daya ne a hannun dan bindiga na da hadari ga al’ummar jihar.

“Yanzu haka, an tura jirage masu saukar angulu na yan sanda domin ceton yaran. Za’a sanar da iyayen yara da jama’a halin da ake ciki game da wannan yunkuri da ake yi,” Matawalle yace.

“Yayinda muke kokarin karfafa tsaro a makarantun mu, na bada umurnin kulle dukkan makarantun sakandare na kwana dake fadin jihar.”

Leave a Comment

%d bloggers like this: