Bayan kwanaki kadan da aurar da diyarta, Gumsu Abacha, a bikin da ba a yi wani babban shagali ba ga gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, matar tsohon shugaban kasar Najeriya ta shiga shagali.

Maryam Abacha ta kasance mace mai kamar maza sakamakon tsayawa yaranta da tayi bayan rasuwar mijinta, tsohon shugaban kasa na mulkin soji a shekaru masu yawa da suka gabata.

Wannan lokaci ne na shagalin murna ga dukkan iyalan. A makon da ya gabata ne aka yi bikin auren Gumsu a gidan Mohammed Abacha dake Abuja.

A ranar Alhamis, Maryam Abacha ta yi shagalin cikarta shekaru 73 a duniya.

Duk da Gumsu ta taba auren biloniyan kasar Kamaru, Bayero Fadil Mohamadou, tuni dai suka rabu, The Nation ta wallafa.

Yanzu haka ita ce mata ta hudu ga Gwamna Buni, wanda ya auri diyar wanda ya gada, Ummi Adama Gaidam a kwanakn baya.

Allah ya albarkaceta da ‘ya’ya 10, 3 mata da maza 7, Maryam Abacha ce matar shugaban kasan najeriya daga 1993 zuwa 1998 lokacin da ya rasu.

Leave a Comment

%d bloggers like this: