A ƙoƙarin da gwamnatin jihar Kano ke yi na kaucewa faruwar garkuwa da mutane a jihar, gwamnatin ta ba da umarnin rufe makarantu biyar da horar da jami’an kiwon lafiya cikin gaggawa.

Wannan umarni yana ƙunshe cikin wani bayani da mai hulɗa da jama’a na ma’aikatar lafiya ta fitar, Hadiza Mustapha Namadi ga manema labarai a ranar Lahadi.

Kamar yadda yake ƙunshe cikin jawabin, sunayen makarantun da abin zai shafa sun haɗa da: School of Health Technology Bebeji, School of Nursing Madobi, da kuma Schools of Midwifery in Gwarzo da ta Gezawa and Dambatta.

aka ba da umarnin rufe makarantun sakandire sha biyu da na manyan makarantu huɗu da ke wajen garin Kano sakamakon cigaba da taɓarɓarewar matsalar tsaro.

Kwamishinan Lafiya, Dr. Aminu Ibraim Tsanyawa, ya bayyana cewa akwai tsare-tsare na yadda ɗaliban za su cigaba da kartunsu.

Mai jawabin dai ya ba wa iyaye da masu lura da yara shawarar da su je su kwashe ƴaƴansu a safiyar wannan rana ta lahadi.

Leave a Comment

%d bloggers like this: