Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa na duniya Sepp Blatter zai ci gaba da fuskantar haramci kan harkokin wasanni har na karin wasu shekaru bakwai, tare da biyan tara na kudade masu yawa kan zargin cin hanci.

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ta tsawaita takunkumi haramta wa tsohon shugabanta Sepp Blatter shiga harkokin wasanni har zuwa shekarar 2028 wato har zuwa nan da shekaru bakwai masu zuwa, matakin da ya shafi tsohon sakataren hukumar Jerome Valcke.

FIFA ta ce wannan sabon hukuncin zai fara aiki daga lokacin da tsohon hukuncin zai kare a watan Oktoban 2021 da kuma watan Oktoban shekara ta 2025.

An kuma ci tarar sama da dala miliyan daya kan tsoffin jamai’an na FIFA da ake zargi da karbar cin hanci na miliyan 23 kudin Swiss kan gasar ci kofin duniya na 2010 da kuma 2014. Sai dai Blatter da Valcke sun daukaka kara kan wannan sabon hukunci.

Leave a Comment

%d bloggers like this: