Hukumar Yaki da Cin hanci da Rashawa ta Najeriya EFCC, ta kama tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha a ofishinsa da ke birnin Abuja kamar yadda jairdar Daily Trust ta rawaito.

Wata majiya daga shalkwatan EFFC ta ce, yanzu haka tsohon gwamnan na shan tambayoyi.

Ana zargin Okorocha wanda ya mulki Imo tsakanin shekarar 2011 zuwa 2019 da wawure kudade da barnatar da su, amma ya ci gaba da musanta haka.

A karon farko kenan da EFCC karkashin jagorancin sabon shugabanta Abdulrasheed Bawa da tsare wani fitaccen dan siyasa a Najeriya bisa zargin cin hanci da rashawa.

Leave a Comment

%d bloggers like this: