Jami’an hukumar yaki da masu almundahar kudi ta EFCC ta kama Ibeh Theophilus Uche, Shugaban 10 Kobo Wine Place da ke Ikotun a Legas tare da mahaifiyarsa kan zarginsa da damfara ta intanet na kudi kimanin Naira miliyan 50 a Legas.

An kama wanda ake zargin dan shekara 28 a Otel din Radisson Blu Anchorage da ke Victoria Island a Legas bayan samun bayannan sirri kan zarginsa da aikata laifi, rahoton Vangaurd.

Yayin amsa tambayoyin jami’an EFCC, Uche wanda ya ke gabatar da kansa da sunaye da suka hada da Rachael Armstrong, Keanu Reeves, Rebekah Schwarzenberger, Keanu Private, Elizabeth Hortman da Stefan Paulson ya amsa cewa yana damfarar mutane ta Bitcoin, sojan gona da sauransu.

Wanda ake zargin ya kuma amsa cewa ya damfari mutane kudin da ya kai Naira miliyan 50 tunda ya fara aikata laifuka a shekarar 2020.

Binciken da EFCC ta yi ya nuna cewa wanda ake zargin yana amfani da asusun ajiyar kudi na mahaifiyarsa a daya daga cikin bankunan zamani wurin karkatar da kudaden da ya ke samu daga laifukan.

Kayan da aka kwato daga hannun wanda ake zargin sun hada da iPhone 11 Pro Max guda daya; iPhone 12 pro max guda daya; Kwamfuta MacBook Pro guda biyu ; Game na PlayStation 5; iPad da karamar wayar Nokia.

Sauran sun hada da mota kirar Mercedes Benz S550 2015 da Lexus RX 350 SUV 2016 da wasu kayayyakin da ake zargin da kudin haramun aka siya.

Za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Leave a Comment

%d bloggers like this: