Jami’in dan sanda a garin Aba dake Jihar Abiya, ya kashe wani abokin aikinsa yayinda yake kokarin kama wani da ake zargi da aikata laifi. Kakakin rundunar yan sandan jihar, SP Geoffrey Ogbonna ya tabbatar da faruwar lamarin, duk bai yi cikakken bayani ba.

An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a Bata Junction, yayin da dan sandan ke kokarin harbin wanda ake zargin amma ya yi kuskure ya bindige abokin aikin nasa.

Shaidun gani da ido sun shaidawa manema labarai cewa ‘yan sandan sun yi kokarin tsare wata mota kirar Jeep mai bakin gilashi suka kuma kokarin tilastawa wadanda ke cikin motar su fito su shigar motarsu ta sintiri.

Wani dan sandan daban da ke cikin motar Jeep din ya yi kokarin rokon abokan aikinsa su kyalle su amma ba su amince ba. Da mutanen da ke cikin Jeep din suka ki shiga motar yan sandan shine daya daga cikin yan sandan ya fito da bindiga ya harbi abokin aikinsa cikin kuskure a maimakon harbin wanda suke son kama wa.

Leave a Comment

%d bloggers like this: